Jihar Kano ta kai kayan agaji Nijar

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Dubban 'yan gudun hijira ne suka tsere daga Najeriya zuwa Nijar saboda hare-haren Boko Haram

Gwamnatin jihar Kano a Najeriya ta aika kayayyakin agaji ga 'yan gudun hijirar kasar da ke jihar Difa a jumhuriyar Nijar.

A ranar Alhamis ne jakadan Najeriya a Nijar, Aliyu Isa Sokoto, ya mika kayayyakin a hukumance ga ministan cikin gida na Nijar, Malam Hasumi Masa'udu.

Mai bai wa Firai Minista shawara ta fannin ayyukan agaji a Nijar, Hajiya Sa'adatu Malam Barmu, ta ce kayan agajin sun kunshi buhunhunan shinkafa 1,200 da na Masara 1,500 masara da kuma barguna 2,000.

Hajiya Sa'adatu ta bayyana cewa akwai kwamiti da aka dora wa alhakin raba kayayyakin ga 'yan gudun hijirar, sannan akwai masu sa ido don tabbatar da kayan sun kai ga wadanda ke matukar bukatarsu.