'Mutane 21 ne aka kashe a harin Gombe'

Karin Mutanen da aka kashe a harin Gombe Hakkin mallakar hoto s
Image caption Hukumomi sun rufe makarantu a Gombe saboda dalilai na tsaro

Rahotanni daga jihar Gombe da ke arewa-maso-gabashin Najeriya na cewa ana ci gaba da samun bayanai na irin kisan da aka yi wa mutane a jihar.

Adadin wadanda suka mutu a harin da ake zargin wasu 'yan Boko Haram sun kai garuruwan Nafada da Ashaka da kuma Bajoga da ke jihar, sun kai mutane 21.

Wani mazaunin garin ya shaida wa BBC cewa ya ga karin gawawwaki tara yashe a kan hanya wasu kuma a cikin ciyayi, kuma dukkansu an yi musu harbi da bindiga ne.

Maharan dai sun kashe wani fitaccen malamin addinin Musulunci da yaransa da kuma wasu sojoji biyar.

Karin bayani