Boko Haram: 'Karbe makamai barazana ce'

Nigeria Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban Boko Haram Abubakar Shekau ya tabbatar suna kwace makamai daga jami'an tsaron Najeriya

Kwararru a Najeriya na nuna fargaba kan yadda masu ta da kayar baya ke ci gaba da kwace makamai bayan sun kai hare-hare.

Kungiyar Boko Haram da ke ci gaba da kai hare-hare a wasu sassan kasar na kwashe makamai a barikokin soji da ofisoshin 'yan sanda.

A harin baya-bayan nan da ake zargin 'yan kungiyar sun kai a jihar Gombe, maharan sun yi waon gaba da nakiyoyi masu dumbin yawa daga kamfanin siminti na Ashaka.

Hakan na kara jefa fargaba a zukatan jama'a bisa tsoron cewa kungiyar za ta yi amfani da su ne wajen kai hare-hare.