An soki gwamnatin Nigeria kan tsagaita wuta

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau ya ce ba su cimma tsagaita wuta da gwamnati ba

Masu fafutukar ganin an ceto 'yan matan Chibok a Najeriya sun bayyana takaici game da amincewar da gwamnati ta yi cewa ba a cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da Boko Haram ba.

A watan Oktoba ne hukumomi a kasar suka ce an kusa sakin 'yan matan na Chibok fiye da 200, bayan an cimma yarjejeniya da kungiyar ta Boko Haram wadda ke tsare da su.

Daya daga cikin shugabannin kungiyar Bring Back Our Girls, Hadiza Bala Usman, ta shaida wa BBC cewa labarin rashin cimma yarjejeniyar wani abin kunya ne.

Ta kara da cewa lamarin ya sa mutane sun yanke kauna da gwamnati.

A ranar Talata ne mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkar tsaro ya ce ba a cimma yarjejeniya da Boko Haram ba.