An ci tarar Shafin Internet na masoya

Shafin Internet na masoya Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shafin Internet na masoya

Mai tafiyar da shafin nan na internet na masoya masu cututtukan da ake dauka ta hanyar jima'i na fuskantar tara ta dola 16.5 bayan ya gaza samun nasara a karar da aka kai shi ta yin kutse a sirrin mutane.

An zargi mai shafin da laifin baiwa wasu shafukkan na sada zumunta hotuna da bayanan sirrin wasu mutane duk kuwa da alkawarin da ya yi cewar ba zai fallasa zirin su ba.

Alkalin wata Kotu ya samu mai shafin dake jihar California da laifin karya dokar abokan hulda da shi.

Haka kuma Kotun ta yanke hukuncin cewar mai shafin ya aikata zamba da keta da danniya.

Tun shekara ta 2011 aka shigar da karar, lokacinda wani wanda ba a bayyana sunan sa ba ya gurfanar da Kamfanin Successfulmatch gaban Kotu - a wani bangare na neman daukar mataki kan sa.

Kamfanin na SuccessfulMatch yana tafiyar da shafukka da dama na sada zumunta tsakanin masoya, sannan kuma yana tafiyar da wani shiri na jagoranci ga wadanda suke neman bude shafin su na kan su.

Kamfanin yana bayar da manhaja da matattarar bayanai dake kunshe da bayanan sirri na daruruwan dubban mutanen da suka yi rajista da shi.

Sai dai kuma takardun Kotun sun yi bayanin cewa shafin na Internet PositiveSingles ya yi tallar kan sa a matsayin dari bisa dari shafin dake boye sirrin mutane.

Kamfanin ya rubuta "ba mu bayyanawa ko sayarwa ko bayar da aron bayanan sirri na wani mutum ga wata kungiya ko kamfanin irin na mu."

Karin bayani