Twitter: An saukaka hanyar aike wa da sako

Twitter Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kamfaniun Twitter ya bayyana canjin ne ta hanyar aika wa da sakona dandalinsa

Kamfanin dandalin muhawara na Twitter ya sauya yanayin shafinsa ta yadda za a saukaka aika wa da sako.

A cewar masu kamfanin, wadanda ke amfani da wayoyin salula wajen aike wa da sako ta Twitter ba za su ga wani canji ba amma masu amfani da kwafutoci na gida za su ga cewa shafin aika wa da sakon mai kalmomi 140 ya dan sauya kadan.

Wato a maimakon ya bayyana a hanun hagu zai kasance a saman sashin timeline.

Ya zuwa yanzu dai babu dalalilin da dandalin na Twitter ya bayar kan daukan wannan mataki.

Kuma neman karin bayani daga kamfanin kan wannan canji ya cutura.

Kamfanin dai ya aika da wannan canji ne ta shafin Twitter kuma babu wani karin bayani da ya biyo baya.

A lokacin da kamfanin ya yi wani sauyi a baya kan yadda za a hada tattaunawa jama'a a wajen dandalin ya janyo cece-kuce a tsakanin masu amfani da dandalin, koda yake daga baya mutane sun yi na'am da canjin.

A baya akwai canjin da aka yi a bangaren samun sautuka da kuma yadda kamfanin ke rufe wasu tsare-tsarensa a watan Disamba, wadanda tuni aka yasar da su.