Uganda ta dakatar da kwamandoji 15

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Dakarun Uganda na cikin AMISOM

Kakakin rundunar sojojin Uganda ya ce an dakatar da wasu manyan kwamandojin soji 15 daga bakin aiki bisa zargin cin zarafi.

Ana ci gaba da bincike a kan zargin cin zarafin da ake yi wa sojojin Uganda da aka tura zuwa Somalia a karkashin rundunar kasashen Africa ta AU watau AMISOM.

Kakakin rundunar, Paddy Ankunda, ya ce wani bangare na binciken da ake yi ya shafi zargin yin lalata da mata.

Wannan mataki ya biyo bayan wani rahoto da kungiyar kare hakkin bil-adama ta Human Rights Watch ta wallafa a watan Satumba.

A cikin rahoton an yi zargin cewar wasu sojoji daga Burundi da Uganda sun yaudari wasu mata da alkawarin basu taimako domin yin lalata da su.