Mutane goma ne suka mutu a harin Azare

Hakkin mallakar hoto no credit
Image caption Mutane na yin layi mai tsawo a wasu na'urorin cirar kudi a Najeriya

Rahotanni daga jihar Bauchi a arewacin Najeriya na cewa akalla mutane goma ne suka rasa rayukansu, wasu fiye da ashirin suka jikkata a harin da aka kai garin Azare.

Lamarin na ranar Juma'a ya faru ne yayin da dimbin jama’a suka yi layi domin hada-hadar kudi ta na’urar ATM ta bankin First Bank.

Harin ya kuma rutsa da ma’aikatan gwamnati da ke kokarin cire kudaden albasinsu a bankin.

Kawo yanzu hukumomin tsaro ba su yi karin bayani game da harin ba.