Takaddama kan wanda ya kashe Osama

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ma'aikatar tsaron Amurka ta Pentagon dai ba ta ce komai ba game da ikrarin na Mr. O'Neil

Wani tsohon sojan ruwa na kasar Amurka ya tayar da sabuwar takaddama kan yadda aka kashe shugaban Al-Qaeda Osama Bin Laden.

A wata hira da Robert O'Neill, ya yi da jaridar Washington Post ta Amurka sojan ya yi ikirarin harbe Bin Laden a gidan da yake boye, a garin Abbottabad da ke Pakistan.

Mr. O'Neill ya yi ikirarin cewa shi kadai ya shiga cikin dakin da shugaban Al-Qaedan ya ke, ya kuma harbe shi a ka.

Wannan ikirari na Mr. O'Neill ya sha bam-ban da ikirarin da wani tsohon sojin ruwa na Amurkan, Matt Bissonnette, ya yi a baya kan yadda aka kashe Osama Bin Laden din.