Sojin Burkina Faso sun yi watsi da wa'adi

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Soji sun karbe mulki bayan hambarar da shugaba Blaise Compaore

Sojin da suka karbe mulki a kasar Burkina Faso sunsun yi watsi da wa'adin da kungiyar Tarayyar Afrika ta basu na mika mulki ga farar hula.

Kungiyar dai ta bai wa sojojin wa'adin makonni biyu ne su mika mulki ga gwamnatin rikon kwaraya wadda zata shirya zaben shugaban kasa a Burkina Faso.

Shugaban sojin laftanal kanal Isaac Zida ya ce "Bama tsoron a sanya mana takunkumi, mun fi damuwa da samun zaman lafiya mai dorewa."

Bayan wani tattaunawa da jam'iyyun adawa da kuma kungiyoyin fararen hula, sun amince da cewa za a yi babban zabe a badi, amma ba su yi maganar mika mulki ga wani da zai jagoranci kasar kafin sannan ba.