An rufe shafukan intanet na batsa 400

Hakkin mallakar hoto THINKSTOCK
Image caption Shafukan ana sayar da miyagun kwayoyi

'Yan sandan kasa-da-kasa sun rufe shafukan guda 400 wadanda ake amfani da su wajen siyar da fina-finan batsa na yara da miyagun kwayoyi da makamai.

Shafukan sun hada da shafin the Silk Road 2.0.

Kazalika, an kama mutane da dama da ke da alaka da wadannan shafuka.

Masu bincike sun ce sun kwace miliyoyin kudaden da ake amfani da su a mu'amalar intanet kawai.

Jami'an tsaro daga kasashen Turai goma sha shidda da kuma hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka, FBI ne dai suka gudanar da wannan bincike.