ECOWAS ta tara kudaden yaki da cutar Ebola

Shugabannin kasashen ECOWAS
Image caption Shugabannin kasashen ECOWAS

A birnin Accra na kasar Ghana cikin daren jiya shugabannin kasashen kungiyar Kasuwancin yammacin Afrika wato Ecowas suka kammala wani taron gaggawa na yini guda da suka gudanar a can.

Sun dai gudanar da taron ne kan batutuwa biyu wato da matsalar cutar Ebola da yadda za'a shawo kanta da kuma alamarin Burkina Faso, inda sojoji suka kifar da gwamnatin Blaise Campaore.

Shugabannin kasashen guda takwas ne dai suka halarci taron ciki har da shugabannnin kasashen Mali da Niger da Ivory Coast sauran kuma suka turo wakilai.

Mallam Haruna Warkani Mataimakin Direkton Sadarwa na kungiyar ta Ecowas ya bayyana cewa Shugabannin sun ba da taimakon kudade da na'urori a kokarin da ake yi na ciwo na cutar Ebola.

An kuma daidaita batun maida mulki ga farar hula dangane da batun juyin mulkin da aka yi a Burkina Faso.

Karin bayani