2015: INEC ta ce babu batun magudi

Zabe a Nijeriya
Image caption Shugaban INEC, Attahiru Jega

A Najeriya a yayin da babban zabe ke karatowa, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC ta sha alwashin kawar da duk wasu hanyoyin magudi.

Hukumar ta ce ta tanadi wata na'ura da za ta hana amfani da katin wani wajen kada kuri'a a zaben na 2015.

Ana dai zargin 'yan siyasa a kasar kan bi hanyoyi na rashin gaskiya domin samun nasara a zabukan kasar.

Lamarin da ya taimaka wajen sa mutane da dama yanke kauna da lamarin zabe a kasar.

Karin bayani