Akwatin renon bakwaini ya lashe kyauta

Akwatin renon jarirai bakwaini Hakkin mallakar hoto mom
Image caption Akwatin renon jarirai bakwaini

Akwatin renon Jarirai bakwaini da ake hura wa ne ya lashe kyautar James Dyson. Wanda ya kirkiro akwatin renon bakwainin ya ce zai jera da kowanne tsari, kuma "ya ci kudinsa" dari bisa dari.

Samfurin akwatin renon bakwainin ne aka zaba a wajen bayar da kyautar James Dyson ta wannan shekarar.

Kudin akwatin da aka yi ma lakani da Mom, ko kusa bai kama kafar sauran akwatunan da a kan yi amfani da su ba wajen renon Jarirai bakwaini.

Wanda ya kirkiro akwatin James Roberts wanda dalibi ne da ya kammala karatu a Jami'ar Loughborough - ya ce yana fata, za a yi amfani da irin wadannan akwatunan da za a samar a kasashe masu tasowa.

Wani kwararre ya ce akwati ne da za a sanya jarirai muddin dai kankantarsu ba ta gaza kaiwa da bakwainin da aka saba gani ba.

Mr Robert yace ya fara nazarin kirkiro Mom din ne a wani bangare na aikinsa na kammala karatu, kuma wani shiri ne na Talabijin ya karfafa masa gwiwar kirkirar akwatin.

Yace, "ina kallon wani shiri ne na talabijin na BBC dangane da 'yan gudun hijira na Syria, a cikin shirin kuma akwai wani sashe da aka nuna jarirai bakwaini masu yawa suna mutuwa saboda wahalhalu na yaki musamman kuma saboda rashin akwatin da za a rene su a ciki da kuma na'urorin da za su taimaka musu su rayu."

"na yi tunanin cewar, lallai yakamata ace akwai hanyar da za a warware wannan matsalar."

Ya kara da cewar kyautar da aka bayar ta fam dubu 30 na nufin cewar, zai iya cigaba da aiki a kan wannan na'ura wadda yake son kaiwa kasuwa daga nan zuwa shekara ta dubu biyu da 17.

An shirya wannan na'ura ne ta yadda za a dauki bangarorinsa, a hada a wurinda ake bukatar aiki da su.

Karin bayani