Mace ce ta kai hari a Azare

Dan sanda yana duba wurinda aka kai harin Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dan sanda yana duba wurinda aka kai harin

Hukumomin tsaro a jihar Bauchi dake arewacin Nijeriya sun bayyana cewa wata mace ce, 'yar kunar bakin-wake, ta kai harin nan na bam a harabar wani banki a garin Azare a cikin jihar a jiya.

Mutane kimanin goma sha hudu ne dai suka mutu a harin, wasu fiye da ashirin kuma suka samu munanan raunuka a cewar rahotanni.

A jihar Adamawa kuma, ita ma dake arewa maso gabashin Nijeriyar, iyayen yara sun fara maida martani ga matakin rufe makarantun jihar, saboda tsoron hare-hare na masu tada da kayar baya.

Iyayen suka ce, Malamai suka ba su shawarar janye 'ya'yansu saboda manya sun janye na su tuni.

Karin bayani