Gaskiya ne City ba ta tabuka komai - Aguero

Man City Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Aguero ya ce Man City za ta farfado nan ba da jimawa

Dan wasan Manchester City Sergio Aguero ya ce sukar da akewa kungiyar na cewa ba ta tabuka komai a wannan kakar wasa gaskiya ne.

Sai dai Aguero ya kara da cewa kungiyar ta City za ta farfado nan ba da jimawa.

Dan wasan ya kara da cewa City na da lokacin da za ta iya daidaita lamarinta.

Manchester City dai suna kasan teburin gasar zakarun turai ne yayin da suke da tazarar maki shida tsakaninsu da Chelsea a gasar Premier.

"Mun fahimci fushin masu sukar mu, kungiyar ta kashe kudi wajen sayen 'yan wasa saboda haka magoya bayanmu na son suga mun tashi tsaye." In ji Aguero.