An rufe shafukan internet na miyagu

Kungiyoyi na Miyagu a Internet Hakkin mallakar hoto ThinkStock
Image caption Kungiyoyi na Miyagu a Internet

An rufe shafin Internet na Silk Road 2.0 da sauran wasu shafukkan dari hudu daka yi imanin suna tallar migayun kayayyaki da aka haramta wadanda suka hada da miyagun kwayoyi da makamai.

Shafukkan suna gudanar da harkokinsu ta fannin hanyar sadarwa ne ta Tor - wani sashe na internet da ba za a iya kaiwa gare shi ba ta hanyar al'ada da ake bi ta neman bayanai.

Samamen na hadin-gwiwa da aka yi tsakanin kasashe goma sha-6 na Tarayyar Turai da Amurka ya sa an kai ga cafke mutane goma sha-7 tattare da Blake Benthall wanda aka ce shine jagoran kirkirar shafin internet din na miyagu Silk Road 2.0

Kwararru sun yi imanin cewa rufe wadannan shafukka wata babbar nasara ce a yakin da ake yi da masu aikata miyagun laifukka ta internet.

An kuma kama wasu 'yan Brittaniya 6 wadanda suka hada da wani mutum mai shekaru 20 da haihuwa dan yankin Liverpool da kuma wani dan shekaru 19 da haihuwa dan yankin New Waltham, da wani mai shekaru 30 da haihuwa dan Cleethorpes da wasu Mace da Namiji dukkansu 'yan shekaru 58 da haihuwa daga yankin Aberdovey dake Wales.

A cewar hukumar yaki da miyagun laifukka ta kasa, an yi ma mutanen tambayoyi kuma dukkansu an yi belinsu.

Sashen na internet na Tor, baya ga kasancewar sa wurinda a kan samu wasu shafukkan na halas, har ila yau, sashe ne da ya kunshi kasunni na miyagun kayayyaki da suka hada da filin tallar miyagun kwayoyi da lalata da kananan yara da kuma sashe na kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi.

Samamen da aka kai a bara ne na rufe sashen tallace-tallacen miyagun kwayoyi Silk Road ya zamo babbar nasara ta farko a yakin da ake yi da masu aiyaka miyagun laifukka ta internet.

A yanzu wannan samamen da ya kunshi kasashe dabam-dabam na duniya ya kai ga sanya yakin ya kai wani sabon mataki, yayinda aka rufe shafukkan dari hudu na internet da suka hada da da Silk Road 2.0.

Yana da muhimmanci a tuna cewar, miyagun shafukkan na internet ba wai kawai suna aikata miyagun laifukka ba ne, hanya ce da kowa ya sani hukumar leken asiri ta Amurka ta kirkiro ta hanyar Tor don taimaka ma ayyukan ta da kuma taimaka ma mutanen dake rayuwa a karkashin mulki na danniya.

Karin bayani