Ebola: Manyan 'yan kasuwa sun yi alkawarin $30m

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Cutar Ebola ta halaka kusan mutane 5,000

Manyan 'yan Kasuwa a Afrika sunyi alkwarin taimakawa da kusan dala miliyan 30 don taimakawa da yakin da akeyi da Ebola.

Sun tara kudin ne Adis Ababa babban birnin Habasa.

Za'a yi amfani da kudin ne wajen biyan albashin ma'aikatan kiwon lafiya kusan dubu daya da za a tura Guinea, da Laberiya da Saliyo.

Kungiyar agaji ta Medecins Sans Frontieres ta ce an samu saukin annobar sosai a kasar Laberia. Kungiyar lafiya ta duniya tace kusan mutane dubu biyar ne cutar ta hallaka a yammacin Afrika.