Facebook na tara kudaden yakar Ebola

Wanda ya kirkiro shafin Facebook Mark Zuckerberg Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wasu dai na ganin cewar fito da sabon madannin wata hanya ce ta tallata haja da Facebook ya tsiro da ita.

Shafin sada zumunta da muhawara na Facebook ya kara madanni ga masu amfani da shafin wanda zai ba mutane damar bada gudummawarsu domin yakar cutar Ebola.

Kudaden dai za su isa ne ga kungiyar likitocin kasa da kasa, da kuma kungiyoyin bada agaji na Red Cross da Red Crescent da kuma asusun kula da kananan yara na Save The Children.

Haka kuma Facebook zai biya wasu kudade domin karfafa shafukan Internet da wayar salula a nahiyar Afurka ta yamma.

Cutar ta Ebola dai ta hallaka kusan mutane 5,000 a kasashen Laberiya, Guinea da kuma Saliyo.

Wanda ya kirkiro shafin sada Zumunta da Muhawar na Facebook Mark Zuckerberg ya sanar da wannan sabon madanni ne a cikin wani hoton Bidiyo da ya wallafa a shafinsa mai taken '' Zan tabbatar da cewa shafin Facebook ya taka rawa wajen yaki da cutar Ebola.''

ko a watan da ya gabata ma Mark Zuckerberg ya bada tallafin dalar Amurka Miliyan 25 domin yaki da cutar.

Sai dai wasu na sukar lamirin Facebook na fito da wanann sabon madanni, a cewarsu ya yi hakan ne domin karawa shafin na sa kasuwa.

Wani mai sukar lamari Pepe Pepe Pepe ya wallafa shafin sa na Facebook cewar shi bai amince da wannan mataki da aka dauka ba, dan haka wannan wani sabon salon kasuwanci ne, in ba haka ba nawa shi Facebook ya bada a matsayin gudumma dan yakar cutar ta Ebola.

Inda nan take Zuckerberg ya maida masa martani da cewa '' Ni a kashin kaina na bada tallafin dala miliyan 25, kuma Facebook zai kashe miliyoyin daloli domin da Internet a kassahen da cutar ta fi kamarai.''