Ana samun raguwar masu cutar Ebola a Liberiya- MSF

Liberia
Image caption A Guinea da Saliyo ana ci gaba da samun masu kamuwa da cutar Ebola

A karon farko, Kungiyar agaji ta Medecins Sans Frontiere wato MSF a takaice ta sanar da cewa a kasar Liberiya daya daga cikin kasashen da cutar Ebola ta fi yin kamari ana samu raguwar wandanda suka kamu da cutar Ebola sosai.

Sai dai kuma Kungiyar ta MSF ta ja hankalin cewa ana samun karuwar wadanda suke kamuwa da cutar a sauren kasashen biyu wato Guinea da Saliyo duk da cewa ana kokarin shawon kan cutar ne a lokaci guda a cikin kasashen uku.

Kusan mutane 5,000 hukumar lafiya ta duniya WHO ta sanar da cewa sun mutu daga cutar ya zuwa yanzu a kasashen uku.

A karshen makon nan ne kungiyar kasashen kasuwancin yammacin Afrika wato ECOWAS ko kuma CEDEAO ta kammala wani taro a birnin Accra na kasar Ghana inda aka amince da daukar sabbin makatan yaki da cutar.

Daga cikin matakan akwai alkawarin kudade da kasashen suka ce za su bayar domin tallafawa yankunan da cutar ta fi kamari.