An kashe direban gwamnan Nasarawa

'Yan bindiga a jihar Nasarawa a Nigeria sun kashe shugaban direbobin gwamnan jihar, Umaru Al-Makura.

Kamfanin dillancin labaran Nigeria -NAN ya bayyana cewa kakakin 'yan sandan jihar Nasarawa, ASP Ismaila Numan ne ya tabbatar da kisan.

Bayanai sun nuna cewar 'yan bindigar sun bindige Malam Abdullahi Mairuwa har lahira a lokacin da ya ke tuka mota tare da iyalansa a kan hanyarsu ta zuwa karamar hukumar Keana a cikin jihar.

Kakakin 'yan sandan ya kara da cewar a gaban matar Mairuwa aka harbe shi da bindiga a kirji lamarin da ya janyo ajalinsa.

Rundunar 'yan sandan ta Nasarawa ta ce ta baza jami'anta domin gano wadanda suka yi kisan.

Kawo yanzu babu bayanai ko kisan na da nasaba da rikicin siyasa a jihar.