APC na korafi kan raba katin zabe

Hakkin mallakar hoto b

Babbar jam'iyyar adawa a Najeriya ta koka da yadda hukumar zaben kasar ke gudanar da aikin raba katin zabe na din-din-din.

Jam'iyyar APC ta ce aikin raba katin zaben ya ci karo da matsaloli a jihohin da ta ke da karfi sosai.

Sakataren yada labaran jam'iyyar, Lai Mohammed, ya ce tun da farko hankalin jam'iyyar bai kwanta ba akan yadda hukumar ta shirya aikin raba katin zaben.

Ya zargi hukumar da hada baki da gwamnatin tarayya domin shirya magudi a zabe mai zuwa.

To sai dai hukumar zaben ta musanta zargin. Mai magana da yawunta, Mista Nick Dazang, ya gaya wa Sashen Hausa na BBC cewa zargin ba ya da tushe.

Ya ce hukumar za ta yi nazarin korafe-korafen da ake yi domin magane duk wata matsala da aka samu wajen raba katin.

A waje daya kuma hukumar zaben ta ce ta kara wa'adin bada katin zaben a jihar Kano.

Sanarwar da ta bayar ranar Lahadi ta ce za a ci gaba da bada katin har zuwa ranar Litinin, maimakon kammalawa a ranar Lahadin.

Hukumar ta ce an dauki matakin ne sabo da jinkirin fara bada katin a ranar Juma'a da aka fara.

Mutane da dama dai a jihar Kanon na korafin rashin samun katin.

Karin bayani