Ana shagalin rushewar bangon Berlin a Jamus

Bangon Berlin a wancan lokacin Hakkin mallakar hoto GETTY
Image caption Ana sa ran dubban mutane za su halarci shagalin a yau.

A yau ne Za a fara shagulgula a kasar Jamus domin tunawa da shekaru 25 da rushewar bangon Berlin, a bangare guda kuma ana gargadin yakin caacr baki da duniya ke ciki.

Ana sa ran dubban mutane za su halarci shagulgulan da za a yi da suka hada da tande-tande da lashe-lashe a kan titunan kasar.

Kusan shekaru 30 bangon na Berlin ya raba birni daya, bangaren iyakar da ke d dan karen tsaro wadda ta raba gabashin Jamus da ke bin tsarin gurguzu daga yammaci, wanda shi kuma ke bin tsarin jari hujja.

Faduwar wannan bango, yau shekaru 25 daidai, wani lokaci ne mai matukar muhimmanci a faduwar tsarin gurguzu, wanda kuma ya share fagen kawo karshen yakin cacar baka.

Daga cikin irin bireden da za a yi har da baje kolin motocin nan da tsohuwar Jamus ta gabas ta yi fice wajen kera su, motar da ake kira trabant a turance.

Ita dai wannan motace da Jamus ta gabas din ta kera sama da miliyan 30 a cikin shekaru 30, amma kuma ba tare da wasu sauye sauye ba na inganta ta.

Motace me kwarin gaske, sai dai tana da shan mai da bulbular da hayaki, ga kuma rashin gudu sosai.

Abin tunawa kuma da wannan mota shi ne, a lokacin da wannan bango na Berlin ya fadi a 1989, ka so ka ga yadda jama'ar Jamus ta gabas suka rika tururuwa a cikinta zuwa cikin Jamus ta Yamma.

Karin bayani