An yi tarzoma a Mombasa

Hakkin mallakar hoto AP

An kashe a kalla mutum daya kuma wasu dadama sun samu raunuka a wata zanga-zanga a birnin Mombasa na Kenya.

Lamarin ya kuma kaiga wawashe shaguna.

Masu zanga-zangar na nuna fushin su ne saboda kisan da 'yan sanda sukayiwa wani mai kaifin kishin Islama.

Sai dai 'yan sanda sun ce ba sune suka kashe Hassan Guti ba, da ake dangatawa da kashe wani babban jami'in dan sanda a watan Ogusta.

An kashe wasu masu tsaurin ra'ayin Islama a Mombasa a 'yan watannin baya.

An kuma zargi Al-shabbab da kai hare-haren bama-bamai a birnin