'Yan gudun hijira na kwarara Kaduna

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wasu da rikicin Boko Haram ya raba da gidajensu

Garin Kaduna ya zama daya daga cikin inda dubban 'yan gudun hijira da suka fice daga Mubin jahar Adamawa da wasu garuruwa da mayakan Boko Haram suka kwace ke kwarara.

Kasancewar hukumomi ba su samar da wani sansani ba na 'yan gudun hijirar a Kadunan, galibin mutanen na zaune ne a gidajen 'yan uwa.

Yawancin 'yan gudun hijirar mata ne da kananan yara, wadanda suka sha wahala sosai kafin su samu tsira zuwa garin na Kaduna.

Wasu daga cikin matan da ke gudun hijirar, sun ce ba su ga 'ya'yansu da mazajensu ba.

Wasu kungiyoyi sun fara ziyartar gidajen da irin wadannan 'yan gudun hijira ke zaune don jajanta musu.

Karin bayani