An rantsar da sabuwar gwamnati a Yemen

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Yemen na fama da rikicin 'yan tawaye

An rantsar da sabon Firai Ministan Yaman da majalisar gudanarwarsa a fadar shugaban kasar, a wani yunkuri na daidaita al'amuran siyasa da kuma tsaron kasar.

Khalid Bahah wanda aka zaba a matsayin Frymijista a watan jiya ya ce zai mutunta takunkuminda aka kakabawa tsohon shugaban kasar, Ali Abdallah Saleh, da kuma wasu shugabannin 'yan tawayen da suka kai hari akan Sana'a babban birnin kasar a watan Satumba.

Sanarwar takunkumin a ranar Jumu'a ta tayarda wani sabon rikicin siyasa.