Rashin tabbas a kan shugaban IS

Abu-Bakr al-Baghdadi Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kungiyar IS na fafutukar kafa daular musulunci a kasashen Iraqi da kuma Syria.

Akwai rashin tabbas kan halin da shugaban mayakan masu fafutukar kafa daular Musulunci na kungiyar IS ke ciki.

Ma'aikatar tsaron Iraqi ta ce an ji wa Abu Bakr al-Baghdadi ciwo, a wani hari ta sama na hadin gwiwa da Amurka ke jagoranta.

Ma'aikatar tace hakan ya faru ne a daidai lokacin da shuagabannin IS suke gudanar da wani taro a birnin Mosul a ranar juma'ar da ta wuce.

Sai dai sojojin Amurtka sun ce har yanzu ba su tabbatar da sahihancin wanann batu ba. Wani Kakakin sojin Amurka yace ba zai iya cewa al-Baghdadi na daga cikin mutanen da ke gudanar da taron ba, alokacin da aka kai harin.