'Mutane 47 sun mutu a Potiskum'

Hakkin mallakar hoto
Image caption Kungiyar Boko Haram a baya ta sha kai hare-hare a makarantu da ke jihar Yobe

Rahotanni daga jihar Yobe a Najeriya na cewa wani bam ya fashe a wata makarantar sakandare ta maza da ke Potiskum.

Wasu wadanda suka shaida al'amarin na cewa akalla mutane fiye da 47 ne suka mutu, yayin da wasu da dama kuma suka jikkata.

Kakakin 'yan sandan Nigeria, Emmanuel Ojukwu ya tabbatar da mutawar mutane 47 sannan 79 kuma sun samu raunuka.

Bam din dai ya fashe ne a yayin da dalibai da malamai ke halartar taron makaranta da safe a ranar Litinin.

Kawo yanzu dai hukumomi ba su kaiga cewa komai ba game da harin, haka kuma babu wanda ya fito ya dauki alhakin kai harin.

Lamarin na zuwa ne mako guda bayan wani dan kunar bakin wake ya kashe 'yan Shi'a masu muzaharar Ashura 21, a garin na Potiskum.