Ana ci gaba da kokarin warware rikicin siyasar Burkina Faso

Laftana Kanar Isaac Zida Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban mulkin Soji a Burkina Faso

Shugaban kungiyar hadin kan Afirka kuma shugaban kasar Mauritania Mohamed Ould Abdel Aziz,na kasar Burkina Faso, a daya daga cikin yunkurin kasashen duniya, na samo hanyoyin warware rikicin siyasar da ke faruwa a kasar.

Shugaba Abdel Aziz ya gana da shugaban rikon kwaryar kasar ta Burkina Faso Laftana Kanar Colonel Isaac Zida.

Laftana Kanar Zida na fuskantar matsin lamba na ya sauka ya baiwa gwamnatin farar hula jagorancin kasar, kafin ya zuwa lokacin da za a sake gudanar da sabon zabe.

A baya dai cikin wannan watan an gudanar da gagarumar zanga-zangar, da ta tilastawa shugaba Blaise Compaore sauka daga karagar mulki, bayan ya shafe shekaru 27 yana mulkin kasar.