Kokarin sulhu tsakanin China da Japan

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wannan ne karon farko da shugabannin su ka yi ganawa fuska da fuska

Shugaban China Xi Jinping da kuma Firayim ministan Japan, Shinzo Abe sun yi tattaunawa a karon farko tun da suka hau karagar mulki shekaru 2 da suka wuce.

Taron gabanin wani taron kolin yanki a Beijing, ana daukar sa kamar wani ci gaba a kokarin warware mummunan zaman dar dar tsakanin kasashen biyu game da hamayyar ikirarin tsibiran da Japan ke iko da su a tekun gabashin China.

An nuna Mr Xi ya yi kikam ba tare da wani murmushi ba a lokacin da suke musabaha.

Yayinda shi kuma Mr Abe din ya fito fili ya furta cewa, wannan ganawa matakin ne da zai kai su ga yaukaka dangantakarsu.