Miji zai biya matarsa $1bn

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shari'ar rabuwar auren na daya daga cikin manyan shari'un aure a Amurka

Wata kotu a Oklahoma ta umarci shugaban kamfanin mai na Continental Resources na Amurka Harold Hamm ya biya tsohuwar matarsa kusan dala biliyan daya don mutuwar aurensu.

Mrs Sue Ann Hamm mai shekaru 56 ta zargi mijin nata ne da neman wata mace a waje, don haka ta nemi rabuwarsu.

Alkalin kotun ya yanke hukuncin cewa attajirin mai shekaru 68, zai rika biyan kudin har dala miliyan 99.5 daki-daki akalla dala miliyan bakwai a kowa ne wata.

Tsoffin ma'auratan da suke da 'ya'ya mata biyu, sun kasance tare sama da shekaru 25.

Akwai damar daukaka kara akan hukuncin na mai shari'a Howard Haralson.