Fasaha na barazana ga ayyuka a Birtaniya

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Wasu masana na ganin ba duk wani aiki ba ne naura za ta iya yi kamar yadda mutum zai yi

Wani bincike ya nuna cewa na'urori za su rika yin kashi daya bisa uku na ayyukan da mutane ke yi a Birtaniya nan da shekaru 20.

Binciken da Jami'ar Oxford ta gudanar ya nuna cewa ayyukan masana'antu da ayyukan akawun ofis da ayyukan tsaro da makamantansu su ne suka fi fuskantar wannan barazana.

Binciken wanda aka kaddamar, ya nuna cewa, tuni aka kama hanyar tabbatar da wannan sauyi.

Masu nazarin sun fahimci cewa ayyukan da ake samun albashin fam 30,000 a shekara na fuskantar wannan barazana kashi biyar fiye da wadanda ake samun fam 100,000.

Rahoton masanan ya nuna cewa ayyukan masu kula da dakunan karatu da masu tallata kayayyakin masana'antu da masu ayyukan kamfanin shirya tafiye-tafiye(eja-eja) da sakatarori tuni sun ragu da sama da kashi 40 cikin dari a Birtaniya tun daga 2001.

Hakkin mallakar hoto AP PhotoThe Hershey Company

A madadinsu yanzu an samu sabbin ayyuka wadanda ba a san sunansu ba ma shekaru goma da suka wuce.

Haka kuma rahoton ya gano cewa kashi 40 cikin dari na ayyuka a Birtaniyan,kamar na bankuna da na kwamfuta da na injiniya da na lafiya da na yada labarai ba sa fuskantar barazana sosai.

Daman tun lokacin da aka samu cigaban masana'antu a Birtaniya ake tunanin za a iya kaiwa ga matakin da fasaha za ta maye gurbin wasu ayyuka.

Kafin shekarun yanzu da dama daga irin wannan bincike ana ganin kamar ana zuzuta su ne.

To amma ci gaban da ake gani a 'yan shekarun nan na kwamfuta ya sa wasu masu nazarin tattalin arziki sauya tunani.