An datse kan masu fafutika a Libya

Mayakan masu tsatstsauran kishin Islama a Derna Hakkin mallakar hoto REUTERS
Image caption Mayakan masu tsatstsauran kishin Islama a Derna

A kasar Libiya an datse kawunan wasu matasa uku masu fafitika a gabashin birnin Derna dake kusa da birnin Benghazi, dake hannun kungiyoyi masu rike da makamai tun a shekara ta 2012.

An sace dukkanninsu ne a cikin farkon wannan watan, kuma an gano gawarwakin nasu a ranar Litinin.

Cikin kungiyoyin dake rike da ikon birnin, akwai wadda ta ayyana mubaya'arta ga kungiyar I-S mai da'awar kafa daular musulunci a Iraqi da Syria.

Masu fafutikar na samar da bayanai kan halin da birnin na Derna ke ciki a shafukan sada zumunta na internet.