2015: Jonathan zai kaddamar da aniyarsa

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption 'Yan jam'iyyar adawa ta APC na zargin shugaban da gazawa a mulkinsa musamman ta fannin tsaro da rashawa

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan zai bayyana aniyarsa ta sake tsaya wa takara a zaben 2015.

Shugaban zai yi bikin kaddamarwar ne a dandalin Eagles Square da ke Abuja cikin tsauraran matakan tsaro.

Jam'iyyar PDP mai mulkin kasar dai ta amince ta tsayar da Mr. Jonathan a matsayin dan takararta tilo a zaben na badi.

Batun sake tsayawar shugaban takara ya haifar da cece-kuce, lamarin da ya sa wasu 'yan jam'iyyar suka je kotu don kalubalantar tsayawar.

Mr. Jonathan ya yi ta jan kafa kafin ya fito ya bayyana aniyarsa ta sake tsaya wa takara a zaben da za a yi a ranar 14 ga watan Fabrairu mai zuwa.