Sojojin Nigeria 315 ne suka tsere Nijar

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wata majiya na cewa tuni aka mayar da sojojin Najeriya

Rahotanni daga jihar Diffa da ke jamhuriyar Nijar na cewa wasu sojojin Nigeria 315 ne suka tsere zuwa jihar bayan bata kashi da 'y'ayn kungiyar Boko Haram.

Sojoji 13 daga cikin sojojin Najeriyar na ci gaba da samun kulawa a asibitin Difa saboda raunin da suka samu a fafatawar.

Sojojin sun gudu zuwa Nijar din ne a tsakiyar makon jiya bayan gwabza fada da 'yan Boko Haram a garin Malam Fatori da ke kan iyakar kasashen biyu.

Wannan dai ba shi ne karo na farko ba da sojojin Najeriyar suka tsere cikin Nijar.