Shekau ya fitar da sabon bidiyo

Shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau. Hakkin mallakar hoto AFP PHOTO BOKO HARAM
Image caption Kungiyar Boko Haram ta dade ta na kai hare-hare a yankin arewa maso gabashin Nigeria.

Shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau, ya fitar da wani sabon faifan bidiyo.

Shekau ya yi barazanar kashe Danladi Amadu wanda ke ikirarin wakiltar Boko Haram a tattaunawarsu da gwamnatin Najeriya.

A cikin bidiyon dai shugaban kungiyar ya sake nanata cewa babu wata yarjejeniyar tsagaita wuta da kungiyar ta cimma da gwamnatin Najeriya.

Haka kuma ya bayyana goyon bayansu ga kungiyoyin masu fafutukar Islama na kasashen waje, ciki har da kungiyar IS.