Shekau ya yi huduba a sabon bidiyo

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shekau ya ce babu sulhu da gwamnatin Nigeria

Shugaban kungiyar Boko Haram a Nigeria, Abubakar Shekau, ya fitar da wani sabon bidiyo, inda ake ganin shi ya na gabatar da huduba a wani garin da ba a bayyana sunansa ba.

A cikin bidiyon an nuna shi sanye da alkyabba da hula da rawani ba kamar sauran bidiyon da ake nuno shi a daji sanye da kayam soji ba.

Shekau kuma ya yi barazanar kashe Danladi Amadu wanda ke ikirarin wakiltar Boko Haram a tattaunawarsu da gwamnatin Nigeria.

A cikin bidiyon dai shugaban kungiyar ya sake nanata cewa babu wata yarjejeniyar tsagaita wuta da kungiyar ta cimma da gwamnatin Nigeria.

Haka kuma ya bayyana goyon bayansu ga kungiyoyin masu fafutukar Islama na kasashen waje, ciki har da kungiyar IS.