An gano kwayar hana zazzabin taifod

Hakkin mallakar hoto SPL
Image caption Kwayoyin cutar da ke haddasa zazzabin taifod

Masana kimiyya a Australia sun gano kwayar halitta wadda da alamu take kare mutane daga kamuwa da zazzabin taifod.

Ana ganin binciken da masana a Jami'ar Melbourne suka yi zai iya kaiwa ga samar da maganin zazzabin da sauran cututtuka(na bacteria).

Masanan sun ce, kwayar halittar tana iya gano kwayoyin abinci mai gina jiki, a jikin kwayar da ke haddasa cutar, kwayoyin da ke karfafa garkuwar jikin mutum.

Shi dai zazzabin na taifod yana kama mutum ne ta sanadiyyar amfani da ruwa ko abinci maras tsafta.

Kuma yana kama mutane sama da miliyan 20 a kowa ce shekara a duniya.

Sannan ya hallaka dubu 600 daga cikin wadanda ya kama, inji hukumar lafiya ta duniya, WHO.