Mata za su zama limaman Coci

Shugaban Cocin Ingila, Archbishop Justin Welby Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaban Cocin Ingila, Archbishop Justin Welby

A karon farko, Cocin Ingila ta ce amince da wata doka wacce za ta baiwa mata damar zama limaman cocin ko kuma Bishop-bishop.

Dokar dai ta samu gagarumin rinjayen 'yan Angilka na London, hakan kuma na zuwa ne shekaru 20 bayan da Cocin ta Ingila ta amince da wannan kudiri ba tare da fara baiwa matan manyan mukamai ba.

Wakiliyar BBC ta ce "ana sa ran nan da shekara mai zuwa, za a fara nada mata a wannan matsayi, yayin da ake kokarin cike wasu gurabe tara da babu limamai."

Shekaru biyu da suka gabata dai an dakile irin wannan yunkuri na baiwa matan mukaman, lamarin da ya dade yana haifar da takaddama tsakanin 'yan Anglika da suke ganin hakan bai sabawa akidarsu ba, da kuma 'yan gargajiya da suke sukar batun nada mata a matsayin Bishop -Bishop.