Kamaru ta kashe 'yan Boko Haram dubu daya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dakarun tsaron Kamaru

Gwamnatin Kamaru ta ce ta hallaka 'yan kungiyar Boko Haram sama da 1,000 a cikin watanni shida da suka wuce.

A cewarta, sakamakon yaki da 'yan Boko Haram, ta yi hasarar dakarunta 33.

Kakakin gwamnatin Kamaru ya ce za su ci gaba da jan daga domin kare kasa da kuma jama'arsu, a don haka ne ma gwamnatin ta kara aika wa da karin jami'an tsaro kan iyakar kasar da Nigeria.

Hare-hare 'yan Boko Haram ya tilastawa dubban mutane tsallakawa zuwa cikin Kamaru da wasu makwabtan kasashe domin tsaron lafiyarsu da dukiyoyinsu.

Rikicin Boko Haram ya janyo mutuwar dubban mutane a cikin shekaru biyar da suka wuce a Nigeria.