Mata 8 sun mutu bayan tiyatar hana haihuwa

Hakkin mallakar hoto ALOK PUTUL
Image caption Ma'aikatar lafiya ta Indiya ta kaddamar da bincike kan lamarin

Wasu mata takwas sun mutu, yayin da wasu fiye da 50 ke jinya a wani asibiti bayan an yi musu tiyatar hana haihuwa a Indiya.

Matan sun fara korafin jin ciwo daga nan kuma sai zazzabi, bayan tiyatar da aka yi musu a asibitin gwamnati da ke kwaryar kasar.

Mata 30 cikin 50 da ke jinyar na cikin wani mawuyacin hali.

Mazauna yankin sun ce likitoci biyu ne kawai ke yin tiyatar a cikin sa'oi shida.