INEC ta sauya shawarar kirkiro mazabu

Image caption Masu sukan shirin sun nemi shugaban hukumar zaben farfesa Attahiru Jega ya ajiye aiki.

Hukumar zaben Nigeria, INEC, ta dakatar da shirin kirkiro sabbin cibiyoyin zabe 30,000 a sassan kasar.

Hukumar ta ce za ta ci gaba da bin tsarinta na baya na tayar da cibiyoyi a cikin cibiyoyin zaben da ake da su domin rage cunkoson masu kada kuri'a.

Mai magana da yawun hukumar, Mr Nick Dazan, ya ce sun dakatar da shirin har sai bayan zaben 2015, saboda rashin fahimtar da wasu suka yi masa.

Mr Dazan, ya ce, ganin cece-kucen da yunkurin ya jawo zai iya shafar ingancin zabe mai zuwa, ya sa suka dauki matakin.

Wasu 'yan kudancin Najeriyar sun zargi INEC da kokarin fifita arewacin kasar ta hanyar shirin domin zaben na 2015.