Jonathan zai yi shelar yin takara

Goodluck Jonathan Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Goodluck Jonathan

Dandalin Eagle square a Abuja ya cika makil da magoya bayan shugaba Goodluck Jonathan domin sauraren shelarsa ta yin takara.

Tuni dai shugaban da mataimakinsa da kuma sauran gwamnoni suka halarci dandalin na Eagle square.

Sai dai wasu kungiyoyin na ganin bai kamata shugaban ya kaddamar da aniyarsa ta yin takara ba kwana daya kacal bayan dalibai akalla 47 sun mutu a wani harin kunar bakin wake da aka kai a makarantarsu da ke Potiskum.

Haka kuma suna ganin rashin dacewar bikin ganin yadda kungiyar Boko Haram ke ci gaba da kwace garuruwa da yankun a arewa-maso gabashin kasar.

Saidai magoya bayan jam'iyyar PDP suna cewa gwamnatin na yin iya bakin kokarinta wajen kawo karshen rikicin na kungiyar Boko Haram.