2015: Jonathan ya kaddamar da takararsa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wasu na sukar yadda shugaban ya yi bikin kaddamarwar kwana daya bayan kisan dalibai 47 a Potiskum

Shugaban Nigeria, Goodluck Jonathan ya bayyana aniyarsa ta sake tsaya wa takara domin neman ci gaba da shugabancin kasar a karkashin jam'iyyar PDP.

Kafin ya fara jawabi dai sai da aka yi tsit na minti guda domin nuna alhinin kisan dalibai 47 da aka yi a garin Potiskum.

Kuma a jawabin nasa ya bai wa 'yan kasar tabbacin gwamnatinsa za ta dauki matakan kawo karshen tashin hankalin da ake fama da shi a yankin arewacin kasar.

Shugaban ya kuma zayyana wasu daga cikin manyan abubuwan da ya ce ya cimma a fannin ilimi da noma da man fetur tare da cimma nasarar rage yunwa da matukar talauci a tsakanin 'yan kasar.

Mr. Jonathan na neman sake tsaya wa takarar ne duk kuwa da cewa wasu na ganin gwamnatinsa ta gaza wajen magance matsalar tsaro da ke addabar arewa-maso-gabashin kasar.

Musamman ta yin la'akari da kubucewar da wasu yankuna ke yi suna fada wa hannun kungiyar Boko Haram.