An rufe titunan Abuja saboda Jonathan

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption An rufe titunan ne domin tabbatar da tsaro

A Nigeria, an rufe wasu manyan titunan babban birnin kasar, Abuja saboda a tabbatar da tsaro lokacin da shugaban kasar, Goodluck Jonathan zai kaddamar da aniyarsa ta takara.

A ranar Talata ne dai shugaban ke kaddamar da aniyarsa ta sake yin takara a zaben shekarar 2015.

Zai ayyana aniyar tasa ne a babban filin birnin, watau Eagles Square.

Don haka ne hukumar birnin tarayyar kasar ta rufe manyan tittunan da ke kai wa ga filin, da ma wasu manyan titunan birnin.

An dai dauki wannan mataki ne domin tabbatar da tsaro a wajen taron da ma birnin.

Hakan dai ya sa an fara samun cinkoson abubuwan hawa.

Karin bayani