Ana yi wa shugaban Zambia jana'aiza

Image caption Tun a makon jiya ne 'yan Zambia suka fara yin layi a gaban gawar Sata

A Lusaka, babban birnin Zambia, an fara yin jana'izar ban-girma ga shugaba Michael Sata, wanda ya mutu a wani asibitin London a watan jiya.

Ya mutu ne dai yana da shekaru saba'in da bakwai a duniya.

Tun daga makon jiya ne 'yan kasar suka rika yin layi a gaban gawar Mr Sata domin yi masa ban-kwana.

Shugabannin kasashen yankin da dama ne ake sa ran za su halarci jana'izar tasa da ake yi a babban filin wasan kasar.

Za a binne Mr Sata ne a wata makabarta da aka ware domin binne shugabannin kasar.

Karin bayani