Bore mai tasiri a Burkina Faso

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Matasa sun ba zama a kan tituna suna bukatar canji

Babbar zangar-zangar da aka yi a Burkina Faso ta janyo hambarar da gwamnatin Blaise Compaore abinda kuma ya maida dalibai suka zama wasu gwarzaye a kasar.

A safiyar ranar 30 ga watan Okotoba, Lassina Sawadogo bai sani ba ko zai mutu a kan titin Ouagadougou kuma bai da masaniya a kan makomar fafutukarsu.

Mr Sawadogo na daga cikin dubun dubatan matasan da suka ta shi tsaye domin nuna adawa da yinkurin gwamnati na sauya kundin tsarin mulkin kasar ta yadda Shugaba Compaore zai tsawaita mulkinsa na fiye da shekaru 27.

"Sai muka ba zama a kan tituna, saboda mun shirya samun nasara," in ji Mr Sawadogo.

'Jarumi'

Bayan makonni ana tarzoma, a yanzu jami'in harajin mai shekaru 40 ya zama gwarzo.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kungiyar AU ta bukaci Kanar Zida ya mika mulki

A Ouagadougou babban birnin kasar, a yanzu matasa na son hira da Sawadogo saboda ana kallonsa jarumi.

Juyin juya halin na kwanaki biyu ya sa an kifar da Mr Compaore sannan wasu fararen hula 32 sun mutu a yayinda daruruwan mutane suka samu raunuka wadanda har yanzu su ke samun kulawa a asibiti.

Tun bayan da ya yi murabus, Compaore ya tsallaka zuwa makwabciyar kasar Ivory Coast kuma har yanzu ana tattaunawa ta yadda sojoji za su maida kasar kan turbar demokradiyya.