Saliyo zata biya diyyar ma'aikatan lafiya

Jami'an lafiya a Saliyo Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Akalla jami'an lafiya 100 ne suka rasa rayukansu sanadiyyar cutar Ebola.

Hukumomin kasar Saliyo sun ce za su biya dala 5000 a matsayin diyya ga iyalan duk wani jami'in lafiya da cutar Ebola ta hallaka sanadiyyar kula da mai dauke da ita.

Cibiyar yaki da cutar Ebola ta kasar tace iyalan fiye da ma'aikatan lafiya 100 da suka rasu za su ci gajiyar wannan diyyar.

Cutar dai na yaduwa a kasar Saliyo kamar wutar daji, inda aka samu karin mutane 300 da cutar ta kama cikin kwanaki uku da suka gabata.

A watan da ya wuce gwamnatin kasar Guinea tace ta fara biyar diyyar dala 10,000 ga iyalan duk wanda ya rasa rasnsa a kokarin taimakawa mai dauke da cutar.

A bangare guda kuma Wata jami'ar Majalisar Dinkin Duniya kan 'yancin samun abinci Hilal Elver, ta ce mutane fiye da miliyan daya a yankin Afirka ta yamma ne ke fuskantar matsalar karancin agajin abinci sanadiyyar bullowar cuta