'INEC ta kasa samar da katunan zabe a Lagos'

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Dubban dubatan mutane ba su samu katunan zabe ba a Lagos

Mutane a jihar Lagos na ci gaba da korafi na rashin samun katin zabe na din-din-din.

Kugiyoyin fafatikar kare hakkin bil adama da babbar jam'iyyar adawa ta APC dai sun zargi hukumar zabe da wani yunkurin hana wasu daga al'ummar jihar Lagos samun katin.

Sai dai hukumar ta ce babu gaskiya daga wannan zargi.

Hakan na zuwa ne a dai dai lokacin da hukumar zaben ta ce ta dakatar da shirin ta na kara yawan runfunan zabe a fadin kasar.

Mai magana da yawun INEC, Mr Nick Dazan, ya ce sun dakatar da shirin har sai bayan zaben 2015, saboda rashin fahimtar da wasu suka yi masa.