Kumbon bincike ya sauka a kan tauraruwa

comet rosetta Hakkin mallakar hoto PA

An yi nasara a tafiya mafi tsawo da sarkakkiya da wani kumbon binciken sararin samaniya mai suna 'Philae' ya yi, kumbon bincken na Turai ya sauka a kan a kan wata tauraruwa mai wutsiya.

Wannan ne karon farko wata na’ura kirar dan Adam ta sauka a kan irin wannan tauraruwa.

Amma masana kimiyyar sun madaukan da ke makale jirgin, a saman tauraruwa mai wutsiyar basu fid da aman wuta ba, hakan na nufin za a iya samun matsala.

Tuni da Philae ya aiko da sakon hotunan yadda yake sauka kan tauraruwa mai wutsiyar.

Jean-Jacques Dordain shine shugaban hukumar binciken sararin samaniyar ta Turai.

Ya ce, “A yau mun nuna kwarewa da fasahar Turai, ko a cibiyoyin bincike, da masana'antu, da hukumomin lura da sararin samaniya, a ko’ina ma. Wannna ita ce kwarewar da ta fi kowacce a duniya, saboda mune na farko.”